ABNA24 : A jiya Lahadi ne shugaban na Ghana ya jagoranci wata tawaga ta kungiyar zuwa kasar Mali inda shugaban rikon kwarya ta kasar ya tarbe shi da kuma gudanar da tattaunawa kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar.
Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi siyasa da kuma matakan da za a dauka nan gaba wajen ganin ba a samu wani tsaiko ba a shirin gudanar da zabe da kuma mayar da kasar bisa turba demokradiyya kamar yadda aka tsara.
Shugaba Nana Akufo Addo dai shi ne shugaban wata kasa ta farko da ya fara ziyartar kasar Malin tun bayan da kungiyar ta ECOWAS ta dage mata takunkumin a ta kakaba mata biyo bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa tsohon shugaban mulkin farar hula na kasar Ibrahim Boubacar Keita a watan Augustan da ya gabata.
342/